2 Mayu 2017 - 15:54
An yi muzaharar yin tir kiran da El-Rufa'i ya yiwa Malam da dabba yau a Kaduna

A yau Talata 2 ga watan Mayu 2017 ne 'yan uwa suka gabatar da gagarumar muzahara ta yin tir da Allah waddai game da kiran da gwamna El-Rufa'i ya yiwa Malam da dabba a yayin wata ganawa da yayi da tashar Talbijin ta Channels. An gabatar da wannan gagarumar Muzahara ne dai a yau Talata da safe a garin na Kaduna..

Babbar birnin jihar ta Kaduna.

Dimbin mahalarta muzaharar da suka hada maza da mata sun rika daga kwalaye dauke da zanen gwamna wanda suke nunawa a matsayin shine dai abin da ya siffan ta Malam,.

Kaduna

Kaduna

Kaduna

Kaduna

Kaduna

Kamar dai yadda aka sani ne shi gwamna El-Rufa'i na Kaduna ya siffanta Jagora Harkar Musulunci a NIgeria Sheikh Ibraheem Yaqoub El-Zakzaky da dabba a wata hira da talbijin din Channels, kuma har ya zuwa yau bai fito ya nemi afuwar abin da yayi ba.